Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels " ....... Gyara zamanta tayi tace "Allah gafarta malam,wallahi ƴaƴana uku a duniya biyu maza ɗaya mace,mahaifinsu buzune,to su mazan shi suka biyo a kyau,abun takaicin da baƙin cikin ita ƴar macen se tayi muni,wallahi duk sa'anninta sunyi aure amma ita tsabar muni ta kasa samun mashinshine"cewar inna cikin damuwa. Wanda aka kira da sunan malam murmushi yayi yace"wato kinaso de ay mata na farin jini kenan dan tasamu itama ta auru ko?"cewar malam. Karya wiya inna tayi tace"aa nifa ba dan ita nazoba har ga Allah nazone akan su mazan,tunda ance guntun gatarinka yafi sari ka bani,to ni su nakeso ay musu na farin jini,ya zamana ƴaƴan masu mulkin nan da manyan attajirannan su dinga ribibinsu,kaga in Allah ya taimakeni suka auri ƴaƴan manyan ayni shar,tunda kyawawane na bugawa ajarida,shine nazo ataimakamin malam"cewar inna cikin marairaicewa. Shi kanshi malamin ya cika da mamakin jin abinda ke tafe da inna amma to ya ya iya tunda abinda takeso kenan. Nan ya faɗa mata nauin sadakar da zatasa yaran suyi,sannan ya bata garin maganin da zasu dinga turarawa ajikinsu,da kuma nasawa aturare in zasu fita. Inna godiya take tana ƙarawa,ta kawo kuɗin aykinshi ta bashi sannan tai masa sallama ta tafi,kai tsaye kasuwa ta fara biyawa ta haɗo duk abubuwan da zaa kai sadakar sannan ta nufi gida ranta fess,dan duk wani burinta ta ɗorashi kan tagwayen ƴaƴan nata maza wanda Allah yay musu kyau kamar su sukayi kansu. Tana isa gida tasamesu suna shirin tafiya gurin training cikin kayan track sute masu kyau armless riga da wando,gashin kansu har kan goshinsu yake zubosu,baƙiƙƙirin se sheƙi yake,zaratan maza masu cikar halittar da duk macwn da tagansu se sun burgeta. Sunsha mamakin ganinta riƙe da daƙwalen kaji a hannunta har guda biyu,Hisham ne ya karɓi kajin yayinda haisam shi kuma ya karɓi jakar hannunta suka ƙarasa mata dasu cikin gidan. Sannu da zuwa sukai mata ta amsa musu fuskarta ɗauke da murmushi tana ƙara yiwa Allah godiya daya bata su,danma ya ragewa abun siga da be bata su a mataba. "inna zamuje msquare ne trainning, kajin yanka miki za'a yine?a yanka kamin mu tafi,dan bada wuri zamu dawoba"cewar hisham yana kallonta. Riƙe baki tayi tace"wuuu rufamin asiri hisham,lokacin cin kaji daƙwale agidannan har guda biyu beyiba tukunna,na sadakane kai ɗaya ɗan uwanka ɗaya maza kuzo ku goge jikin ku da wannan goron se asa acikin leda ku haɗa da kajin,kai kaba kuturwa,tamace sadaka,shi kuma haisam yaba makauniya me goyo sadakar nashi"cewar inna tana kicikicin kwant goron acikin leda. Cike da mamaki hisham ya kalli haisam,kusan atare suka haɗa baki wajan tambayarta,"inna sadakar a mecece?Kuma mu ina zamuga makauniya me goyo da kuturwa?"suka faɗi suna kallonta. Murmushi tayi tace"na menene kuwa biyulle inba na farin jiniba,ko tunaninku zan baku abinda ze cutar dakune?Kuma makauniya da kuturwa kuna zuwa kano road gasunan jikin masallacinnan har jikin cocin taiwo road sune zaune dan haka da kunje ba wiya zaku samesu."cewar inna. "inna bayan farin jinin da Allah ay mana duk inda mukayi sonmu akeyi,shine yanzukika fara bin malamai danmu,?"cewar hisham. "farin jinin talakawaba,wanda suke jira ku samo ku basu, to tirr da wannan farin jinin ni bashi nakesoba,so nake yau ace kai kana auran ƴar minista,ko shugaban ƙasa,shima ace haka,bawai tarkacen ƴanmata ƴaƴan talakawan dake faɗa akankuba"cewar inna tana kallonsu. Hisham ze sake magana haisam ya dakatar dashi da cewa"innafa gaskiya take faɗi,dan haka akwai buƙatar muma muyi sama gaskiyar innane,yazu ya zaayi da kajin inna in munje gurin almajiran?"cewar haisam yana kallon ɗan uwan nasa. "yauwa ɗan albarka,da kunje gurinsu basu kawai zakuyi da sunce Allah karɓa tofa shikenan sadakar tayi"cewar inna. Miƙo musu goron tayi kowa ya goga ajikinshi,sannan kowa ya ɗauki kazarshi sukai mata sesun dawo,tai musu fatan alkhairi,suka haye mashin ɗinsu haijou fara hisham yaja suka fice agidan. A kan hanyarsu hisham yace "wai da gaske zuwa zamuyi mukai sadakar?Nifa gaskiya ban yarda da wannan tsubbunba ba zuwa zanyiba" Dariya haisam yayi yace"kaimade hisham to ni ɗin cemaka akayi kaiwar zanyi,kawai dan ta barmu mu fito da wurine yasa nayi hakan,yanzu in ka isa gurin ɗan audu me nama na kan kwana ka tsaya mu bashi kajin ya gyara mana,su,inyaso in muka,dawo daga training semu biyo mu karɓa"cewar haisam. Ayko hisham dariya yayi me rai da lafiya ayko ya faka agaban tebur ɗin ɗan audu suka miƙa mishi kajin,sukace yay musu gashin inji suna dawowa,biyanshi kuɗinshi sukayi sannan hisham yaja mashin ɗin suka nufi msquare dan sun kusa yin latti. " " Basu dawo gidaba se bayan ishai,suka tsaya gurin ɗan audu suka karɓo gashin naman nasu,sannan suka sayi lemo me sanyi suka nufi gidan. A tsakar gida suka samu inna da da ƙanwarsu badia,suna cin abincin dare,tabarma badia taje ta ɗauko musu ta shimfiɗa suka zauna suna yiwa inna ya gida. Ta amsa cikin sakin fuska,sannan ta tambayesu batun sadakar in sun samu sunyi. "aybinna muna zuwa ba wahala muka gansu muka basu,muka wuce"cewar hisham yana murmushi. Miƙa mata ledar kajin da lemon haisam yayi yana faɗin"kuma inna daga dukkan alamu sadakar nan ta fara ayki domin wannan kajine wata budurwar hisham ta bamu,gidansu nanan ta wajan msquare ba laifi akwai kaya hannun babanta"cewar haisam ɗin yana dariya. Ayko inna da sauri taja ledar tana faɗin"kun gani ko ay dama malam yace farin jini se kun dinga gudu,sabida matan da zasu dinga sonku kuma ƴaƴan masu kuɗi,Allah nagode maka yau mune da daƙwalen kaji haka agidannan"cewar inna tana yago tsoka ta jefa abakinta ta lumshe ido tana taunawa tana jin wani daɗi aranta. Haka inna taja ta kasa taba kowa nashi suka ci sukasha ruwa tana ta sawa buduwar da akace ta bada kajin albarka,dan sosai naman yay mata daɗi. Haka su hisham suka wuce ɗakinsu suna dariyar santin inna,"haka kawai gida be ƙoshiba kice wai akaiwa kuturwa"cewar haisam yana dariya. To haka inna ta dinga sasu fesa turaruka,namagani wai azuwan zesa su samu ƴaƴan masu kuɗi su sosu, Layu ko data karɓo musu Allah yay yawa dasu wanda duk tarkacen datake basun basa amfani dashi tarasu ske awani buhu acikin ɗakinsu,wanda ita zatonta komai ta basun sunayi. Sun fahimci in har zasu nunamata basu da raayin yin abinda take sasun bazasu shirya da ita bane yasa suke nuna mata sunayi dan su zauna lafiya. ******** "Na rantse da girman Allah duk shegen da ya kuma sawa d'a na ido a layin nan se yasan ya saka,uban wa ya haifamin yaran da zan zauna ay ta sukarmin su,kyaune Allah ne ya basuvba wani shegenba,bare a kwace"cewar inna dake ta faman zage zage atsakar layi,makwabta duk sun leko suna kallonta.Sabida wata makwabciarsu taje tana faɗin wai inna jari takeson yi da ƴaƴanta maza dan taga suna da kyau, Shine maganar ta dawo kunnen innar ta fita tsakar layin tana ruwan bala'i Seda tayi masifar ta iya masifa sannan ta kad'a kanta ta koma cikin gidanta dan ta fahimci zama cikin irin unguwannin nasu dole se ka zama jan wiya za'a dai-daita. A zaune ta samu badia tana wanke wanke tana share hawaye,dan tunda inna ta fita tsakar layin take kuka.karasawa kusa da ita tayi ta dafata tace,"ay ke badia ko kadan baki biyo halina ba,dan da kin biyo halina to wlh da da kudi akace suyi min haka bazasuyi ba,dan sun san inada budurwar ƴa ƴar bana bakwai da zataci ubansu hankali kwance" ,D'ago ido tayi takalli mahaifiyar tata tace cikin taushin murya,"inna to meye ribar yin fad'a da mutane kullum,be da wata fa'ida,kullum cewa kike kinaso kiga nayi aure,inna waye zezo to ya aureni tunda ke abun faɗa baya miki kaɗan yanzu seki fita tsakar layi ki tayi ana kallonki akan abinda bekai ya kawoba"ta fadi tana kokarin mik'ewa.Da kwanukan data wanke "Dalla can rufemin baki sallamammiya kawai,munin kine ya hanaki aure ba halinaba,kuma konki shigarmin faɗa ko kar ki shiga ni kaɗai ma zan iya da kowanne ɗan iska,daɗinta kuma bake kaɗai na haifaba,"cewar inna cikin jin haushi. Murmushi tayi sannan tace cikin ladabi"inna ta takaina Allah yabar min ke,batun gaskiya inna,gwanda daban fita na shiga ba sabida kinga su ajebo kowa yasan basa ji,kuma ina shiga suma shigarwa mamansu zasuyi in mukayi rigima cewa za'ayi tafiyata d'aya dasu shine kawai yasa na hakura ban shigar mikinba tunda beda amfani shi kanshi faɗan"cewar badia a ƙoƙarinta nason kawo ƙarshen maganar dan batason tai tsayi tunda taji inna ta fara ambaton muninta ne ya hanata auruwa. Kwafa inna tayi sannan tace"can ta cakalkale maki,Shiyasa su biyulle ke burgeni basa barin kota kwana,ni ɓace min da gani sullutuwa kawai,nan na siyo mikinman bilicin amma fafur kikaƙi gogawa,nasan da kin shafa da tuni ma inajin mijin yasamu"cewar inna tana balla mata harara Ɗan rusinawa tayi tace"Allah ya huci zuciyarki inna ta"tana gama faɗi tasa kai ta wuce zuwa ɗakinta tunda ta gama wanke wanken Badia tunda ta shige d'aki take share kwalla dan inda sabo tasaba da faɗan na innar tata. Su hishamne suka shigo ɗakin da saurinsu rai aɓace suka ƙarasa gun badia,hisham ɗinne yace yana huci"ukuti yanzu mukacdawoninna ke cewavwai su ajebo sun muku taron dangi,sun zagi inna ta uwa ta uba da gaske ne?"ya tambaya yana huci. A hankali badia ta kalli ƴan uwan nata tace"bada da gaske bane ya hisham amma ay kunsan halin inna dan Allah kar kuce nice na faɗi"ta faɗibatsorace tanaleƙen ƙofar shigowa ɗakin,murya ƙasa ƙasa ta faɗa musu aynihin abinda ya faru. Jinjina abun sukayi aransu dan su inna harda kukanta take faɗa musu irin cin zarafin da su ajebon sukai mata. Da ikvsun riga dasun san wacece inna da abinda takeso hakanne yasa sukayo waje ransu aɓace suna faɗin"Wlh basu zagi banza ba duk shegen daya kwana lafiya shiyaso,dan haka bari muje muga uban daya tsaya musu" Inna na zaune taga shigewarsu da sauri,ay bata tsaya ɗaukar mayafi ba ta biyo bayansu da gudu tana gyara ɗaurin zaninta tana faɗin"maza jarumai na,masu share kuka na,karku barsu sekun rama min, maza kuje ku ƙwato kimar gidanku" Kwanar gidan su ajebon suka shiga suka tsaya wandavita innar azatonta gidan sukaje shiyasa ta tsaya aƙofar gida tana jiran dawowarsu dan har ga Allah abinda sukayi raji daɗinshi,tabbacin tana da zaratan ƴaƴan da bazasu bari awulaƙanta musu itaba kenan. Sun ɗan jima akwanar lungun sannan suka fito suka nufo gida suna huci kamar gaske. A k'ofar gidan suka samu inna tsaye tana masu abunnan da akewa k'auraye"chau chau nawa,Allah de ya biya yan maza,"murmushi sukayi haisam yace"ay munje munci uwarsu inna" Jan su tayi zuwa cikin gida tana murna,badia ko koda suka shigo cikin gidan bata fito ba zamanta tayi aɗaki. " " *FARKON LABARI* Malam Hassan dattijone d'an kimanin shekaru sitti da biyar,buzune daga niger amma zama ya kawoshi jihar katsina awani gari da ake kira mashi. Matar shi d'aya me suna hajara yaransu na ce mata inna, suna da ƴaƴansu uku maza biyu tagwaye,se gambonsu badia,,tun daga kan badia inna ko ta samu ciki sede ya zube,har daga karshe ma bata kara samu ba. So na gidan duniya inna ta d'orashi akan ƴaƴanta,ko ƙuda akan dole yake taɓa mata su,amma dan wani mutum na layi binka zatai har gida taji baasin dukar mata ɗa,ko zaginshi,musamman tagwayen nata da Allah yy musu kyau tamkar indiyawa.. Shekarun ƴan biyun goma aduniya ita kuma badia huɗu Allah yaywa mahaifinsu rasuwa. Duk ɗawainiyarsu seta dawo gun inna,dan taki ba kowa ƴaƴan,ta yarda ta fita tai aykatau ta kawo musu abin bukata.Akan ƴaƴanta,zata iya cin mutuncin kowaye daya taɓa mata su. Tun kan rasuwar malam yake jan kunnenta bisa mugun son da take nunawa ƴaƴan amma tayi burus abunta. Mutanen anguwa har sun ganota,shiyasa ko ina gulmarta sukeyi ita ko ko ajikinta. Ƴan biyunta yara ne masu jini ajika dabasa barin kota kwana,sha yanzu magani yanzu,saɓanin badia da kwata kwata bata son damuwa bare tay hayaniya,rayuwarta cike take da sanyin hali. Uwa uba nunamata wariyar a inna takeyi atsakaninta da ƴan uwanta na ƙara sawa taji bata son shiga mutane tunda taga uwarta ma hantararta takeyi inaga kuma mutanen waje A kwai shak'uwa me k'arfi tsakanin haisam da hisham ,shiyasa ɗaya be jure a wulak'anta masa d'an uwa be d'auki mataki ba. A b'angaren kulawa da iliminsu kuwa inna na iya bakin k'ok'arinta wajen ganin sun samu ilimi wadatacce,har zuwa yanzu da suke kadpoly. Inna ta tsaya tsayin daka,dan ganin y'ay'anta sun haska a duniyar ilimi,hisham nada k'ok'ari sosai,yayin da haisam kuma se anci kwakwa yake fahimtar abu musamman lissafi,amma duk da haka yana ƙoƙari. Haka rayuwarsu ta kasance,suna matukar k'aunar junansu sede ita badia ba me son tashin hankali bace yasa inna ke hantararta,dan tafison su ƴanbiyu dan gani take sune suka gadota faɗa,tunda suna shigar mata.. BAYAN SHEKARU BIYAR. Sanye yake da farar rigar ma'aikatan lafiya,hannunshi rik'e da wasu takardu,ya nufi wani office cikin sauri. Hisham hassan mashi kenan,matashin likita d'an kimanin shekaru talatin da haihuwa. Koda shigar shi office d'in mutanen dake ciki suka mik'e da sauri suka had'a baki gurin fad'in."likita ya ake ciki ta haihu?" Goge gumi yayi sannan yace"Gaskiya sede kuyi hak'uri amma ayki za'ayi mata,dan d'an a gicciye yake munyi iya yinmu abun yaci tura,yanzu zaku bada kud'in ayki dubu ɗari sannan ku kawo jini leda uku,"ya faɗi yana zare farar rigar saman daya ɗora. Jiki asanyaye wani wanda nike kyautata zaton shine mijinta yace,"likita a taimaka mana don Allah,wallahi bamu da dubu ɗari,amma za'a samu dubu hamsin,agurinmu,ataimakemu jinin kuma adebi nawa" Ɗan nazarinsa hisham yayi sannan yace "ba damuwa,Allah ya bata lafiya" Takarda ya rubuta musu suka sa hannu sannan suka je suka biya kuɗin,shi ya cika musu dubu hamsin din,suna ta masa godiya. Minti talatin ya kwashe yayin gudanar da aykin sannan ya kammala,yaciro yaro namiji sankacece. Seda ya tabbatar komai lafiya sannan ya fara shirin komawa garin su,wato kaduna,dan a gwanin gora ne asibitin da yake aykin wanda asibitin gomnatine na garin,yana daukar albashin dubu ɗari biyu da hamsin duk wata, Da albashinshi yaci gaba da ɗaukar nauyin gidansu sabida lokacin shi haisam be samu aykiba tukunna,tun bayan kammala karatun nasu. Abubuwan nayiwa hisham yawa,sabida tun samun aykinshi inna ta dena neman kud'i,acewarta lokacin hutuntane yazo.Shiyasa ta sakar masa komai. Da la'asar ya iso gida,akan mashin ɗinshi wacce ake sata a caji.wanda da k'yar inna ta barshi ya siya acewarta lokacin siyan beyiba. A tsakar gida yasameta,duƙawa yayi har ƙasa yace"inna ta barka da gida ya rana?" Murmushi tayi sannan tace"sannu da zuwa hisham,ina nan nayi tsuru ance hanyar gwanin gora an yanka wani,hankalina duk ya tashi nace to Allah dawo da hisham lafiya" Murmushi yayi yace"eh inna nima ina gun ayki naji ana labarin Allah de yakawo kwanciyar hankali aƙasarmu baki ɗaya"ya faɗi yana kallon agogon hannunshi "Ameen"cewar inna. Daga haka suka ɗan taɓa hira,sannan ya miƙe yashige ɗakin su shida haisam domin yaɗan kintsa. " " Yau asabar hisham baya zuwa ayki,yayin da shi kuma haisam be zuwa ko ina suna gida. Zaune suke a ɗakinsu suna hirar rayuwar duniya,haisam ya ɗan gyara zama yace. "Bross wai don Allah se yaushe zaka yi aure ne?wallahi bana son ganinka a haka 30 years no be beans fa,unda kai ka samu ayki zuwa yanzu yadace ace ka yunƙura,"ya ƙarasa maganar cikin alamun damuwa. Murmushi haisam yayi sannan yadafa kadaɗar ɗan uwan nasa yace."haisam komai lokacine,nima inaso inga nayi auren amma matsalar bazanyi aure ba tare da kaima zakayiba,kuma gashi albashin bekai ya kawoba bare ace ze isa mui mu biyu,sanna kasan duk bin malaman da inna takeyi tana yine dan mu auri ƴaƴan manya,kagako ay ɗaɗɗago aure yanzu aguna ay ba wasa bane"cewar hisham. Tsaki haisam yayi sannan yace"wallahi hisham kana da matsala,yanzu shikenan dan tace haka se ka ƙi yin aure,wallahi tun wuri kasamu mace ka aura,ƙimar ka setafi ƙaruwa a idon duniya da gun Allahma,sannan ay laifin innar ne me yasa ta auri babanmu ayda seta auri me kuɗi,kaga da muma ƴaan masu kuɗinne ay ba wahala zamu samu masu kuɗin" Dariya hisham keyi harda tuntsurawa,sannan yace"Zamuyi aure ɗan uwa in munada rabon yi kaidai katayamu da addu'a"cewar hisha yana murmushi. Hirar su suka ɗan taɓa,sannan suka miƙe dan su shirya tafiya ɗaurin auran ɗan ƙanin babansu,da za'ayi a wani gari me suna marabar rido dake can kusa da nifanari dake kaduna. Ƙarfe biyu agarin na marabar rido tai musu,kowa yasha fararen kaya,se gaisawa suke da ƴan uwa da abokan wasa. Angonne yashiga tsokanar suyana cewa"wallahi ƴan uwa wannan azumin in yazo bakuyi aureba semun kaɗa muku kiɗan gwauro" Gaba ɗaya gurin dariya suka sa musu,wanda su ko murmushi suka yi kawai. Suna nan tsaye lokacin ɗaurin aure yayj suka ɗunguma zuwa gidan sarkin garin wanda amaryar ƴace agurinsa. Bayan ankammala ɗaurin aurene,tawagar angwayen suka ɗunguma zuwa gidan da amarya take da ƙawayenta dan agaisa kuma ayi hotuna. Bayan sun fito an gaggaisa ne idon hisham ya hango masa wata kyakkyawar farar yarinya tsaye can ɗan nesa dasu sanye da irin kayan da k'awayen amaryar suka sa,sede ɗinkin dake jikinta shi ze nuna maka cikakkiyar ƴar birni ce ita kuma wayayyiya, Kunnenta sanye cikin airpod,yayin da hannunta riƙe da wayarta kirar iphone 17,Ta haɗu iya haɗuwa,gata da sassanyar murya,tunda ta gaishe su so ɗaya bata ƙara magana ba,yarinyar akwai class ba ƙarya. Gaba ɗaya hankali da tunanin hisham yatafi kanta,yayin da zuciyarshi ta kamu da zazzafar ƙaunarta a lokaci guda. Amaryarce me suna zainab ta ɗan ƙara matsawa kusa da angon nata tace "yaya Safiyyar kano fa tazo itama," Murmushi angon me suna kabeeru yayi sannan yace"Safiyya manya,ay na hangota ta wani ci magani irin ba wasan nan" Dariya sukayi,sannan Zainab ta waiga ta kira ta,da sauri hisham ya waiga dan yaga wacece Safiyyan. A hankali cikin takunta na ƙasaita ta iso gun amaryar fuskarta ɗauke da murmushi daya ƙara ƙawata fuskarta,ta kamo hannun amaryar tace cikin sanyin murya,"bestie me, ya akayi ne?" Murmushi amaryar tayi tace "naga kin kame a kwana ne shine yasa nace bari in kiraki kizo ku gaisa da yaya da ƴan uwansa dasu kazo daga cikin kaduna,"ta ƙarasa maganar tana kallon su hisham tana dariya. Shiko tunda ta ƙaraso gunsu ya rasa natsuwarshi,shiyasa bema san me ake ba.saɓanin haisam wanda ke ankare da hali da yanayin da ɗan uwan nasa ya shiga sakamakon zuwanta gurin. Hankalinshi be dawoba seda yajiyo muryar amaryar tana faɗin,"Safiyya wainnan sune hisham da haisam twins ne ,babansu sinior brothern baban yaya ne,dsame mother dsame father"cewar amaryar tana gabatar dasu Ɗan Duƙawa ƙasa tayi sannan tace ad'an kunyace"Ya hisham barka da warhaka"cewar safiyya. Murmushin jin daɗine ya kubcewar hisham,da sauri ya amsa mata da cewa"barka de,kina lafiya?" "Lafiya lau"ta bashi amsa. Tana gama gaisheshi tagaida haisam da angon sannan ta wuce zuwa cikin gida wanda shi sam hisham beso hakanba. Basu jima sosai ba sukai musu sallama suka koma cikin gida, su kuma tawagar ango suka nufi motocinsu,har sun shiga mota,haisam ya ɗan ɗauki excuse,ya fita be jima ba ya dawo suka tafi. Tunda suka taho hisham ya rasa meke masa daɗi,gashi be amshi numberta ba har suka rabu,shi de daga uhm she uhm uhm har suka iso kaduna. Wasa wasa hisham ya rasa natsuwarsa kullum da tunanin safiyyaa yake kwana yake tashi, gashi shi irin mutanennan ne masu zurfin ciki,bare ya Sanar da da wani ya bashi shawara. Cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya ya gama fita hayyacinshi da tunanin safiyya,musammam in ya tuno yadda mazaunanta ke juyawa data juya zata koma cikin gida burarshi har tsartuwa take masa. Duk halin da yake ciki hasam na lura dashi,ya fahimci so ne ke dawainiya dashi wanda har ya fara tausaya mishi. Zaune suke suna hira irin ta ƴan uwa,haisam yacewa hisham "ɗan uwa kana cikin damuwa amma ka kasa sanar dani ko wacce irice,shin hakan da kayi dede ne?" Murmushi hisham yayi sannan yace "ko kaɗan haisam hakan be dace ba,amma na rasa ta yadda zan fara sanar dakai ɗinne amma kayi haƙuri" Ajiyar zuciya haisam yayi sannan ya miƙe ya sa hannunsa acikin aljihu ya ciro wata takarda ya cillawa hisham ɗin sannan yace"Gata nan ta amfaneka dan nasan zeyi wiya in ba itace maganin damuwarka ba"yana kaiwa nan ya sa kai ya fice daga ɗakin.Yana murmushi " " A hankali hisham ya ɗauko takardar yana dubawa Safiyya ishaq shine sunan daya gani an rubuta a takardar ƙasan sunan kuma ga numbar wayarta. Sunan nata kawai daya gani hisham ji yayi kamar shawagi yake a sararin samaniya tsabar farinciki Rasa abinda zeyi yayi,tabbas yasan numbarta haisam yasamo masa,to amma in ya kirata me ze ce mata?shine damuwarsa. Kwanciya yayi akan gado sannan yasa numbobin a wayarsa ya danna kira,cikin sa'a ko ta shiga,ba'a jima ba yaji sautin muryarta,tana masa sallama,lumshe ido yayi sannan ya buɗe,bakin da yay masa nauyi da kyar ya amsa sallamar sannan ya ƙara da. "Safiyya kina lafiya?" Jin muryarsa sosai safiyaa ta firgita,dan ko a mafarki taji ta zata iya ganeta,dan tun da ta ɗora idonta akanshi a ranar da suka haɗu Allah ya jarabceta da sonshi,sede ta rasa yadda zatayi taga ta samu damar sake ganinsa.asanyaye ta amsa masa"lafiya lau yaya hisham,ya kukaje gida?" Hisham jin ta ambaci sunanshi seda ya miƙe zaune,ya cire wayar akunnensa ya kalla sannan ya sake mayarwa yace"ya akai kikasan ni na kiraki?" murmushi tayi sannan tace"Yaya haisam ne yace ka turoshi inbaka numbata,so lokacin wannan sabon layine ba wanda yasanni dashi har kama i yanzu in ka cire relatives ɗina shine yasa"ta faɗi tana murmushi, shima murmushin yayi,azuciyarshi yana godewa Allah daya bashi haisam amatsayin ɗan uwa dake gane abinda yake da buƙata batare daya furta ba.amma afili cewa yayi"Allah sarki,da har na ɗauka ko duba kika fara"dariya tayi meɗan sauti sannan tace"rufamin asiri in mutu maza su kaini ba mata ba"gaba ɗaya dariyar sukayi sannan hisham yace "Safiyyaa inason ganinki,dan akwai maganar da nike son yi dake amma bata waya bace,dan akwai buƙatar mu hadu tukunna," Dogon numfashi taja sannan tace"to ya hisham,duk sanda ka shirya ina gida,kuma ina maraba da zuwanka" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace"nagode sosai Kuma insha Allahu cikin week ɗinnan muna nan tafe," Daga haka hira suka ɗan taɓa kaɗan wacce

Chapter 1 of 3