Share this page
2 / 3
yawancinta tambayoyi da amsa ne.daga bisani sukai sallama. Cike da nishaɗi hisham ya lalubo haisam a waya,ya buƙaci ganinsa,ba jimawa ya shigo ɗakin fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Angon Safiyyaa ya akayine?"hisham be bashi amsa ba illa iyaka janyo shi da yayi ya rungume yana faɗin"Bani kai amatsayin ɗan uwa na ɗaya daga cikin baiwar da Allah yay min,haisam nagode sosai,Allah ya bani ikon saka maka"ya faɗi yana rungumeshi Shima rungumeshi yayi yana faɗin"duk wanda yasamu ɗan uwa kamarka ya kasa faranta ransa ya hisham to lahirarsa da kallo"gaba ɗaya suka tuntsire da dariya sannan suka samu guri suka zauna,hisham yafara da cewa."haisam munyi magana da safiyya kuma ta amince da na ganta,sede inda matsalar take kasan farin sani inna bazata barni inje kanoba gunta musamman in tasan ba ƴar kowa bace itan"ya faɗi kamar zeyi kuka. Murmushi haisam yayi sannan yace"ɗan uwa in Allah fa ya baka uwa irin inna to dole ne fa kaima kazama wayayye ta yadda zaka iya bi da ita ba'a samu matsala ba,dan haka kawai cemata zakai seminer zakaje ta yini guda ko kwana ɗaya,abune daya shafi aykinka,kaga shikenan seka fece abunka"duka hisham yakai masa suna dariya,da wannan shawara ta haisam yay ayki inna ta barshi harda binshi da addu'o'in adawo lafiya. Ranar jumma'a ya shirya cikin shiga ta kamala ya wuce garin na kano. Da misalin ƙarfe biyu na rana ya iso kofar gidan nasu safiyyaa,wanda da taimakon waya ya gane. Da fara'arta ta fito domin tarbarsa,bakinta ko rufuwa bayayi,faɗi take "ya hisham ko a mafarki ban zaton sake ganinka ba,sannu da zuwa,kasha hanya"murmushi yayi me ɗaukar hankali yace"se kuma gani azahiri ba amafarkiba"ya faɗi yana kafeta da idanunsa. "Shigo de daga ciki yaya na,na barka a tsaye"cewar safiyya tana dariya. Juyawa tayi zuwa cikin gidan yayin da shi kuma ya mara mata baya cikin tafiyarshi me ɗaukar hankali ta cikakkun maza,a sit room ta ajiyeshi,inda komai an tanadar masa na motsa baki. Bayan sun zauna gabatar masa da abinci tayi,duk yadda ytaso taƙi cin abincin seda modibbo yasa ta suka ci tare, akunyace tasa hannu suka ci. Bayan ya kammala,sun dan natsa ne,ya tattaro duka hankalinsa kanta inda ya fara magana da cewa"Safiyya ni de sunana hsham hassan mashi kamar yadda kika sani, ,nayi makaranta tun daga primary school har zuwa degree dina a kaduna state,inda a yanzu ni karamin likitane a wani kauyen marabar rido dake garinmu,shekaruna 30,ban taɓa son kowa ba bare akai ga batun aure,tunda Allah yasa na fara ganinki safiyya naji kin tafi da duk wani nishaɗina,Allah ya jarabceni da matuƙar ƙaunarki,don Allah ki tausayamin ki soni kamar yadda nake sonki"yaƙara sa maganar cikin raunin murya. Tunda ya fara magana safiyya wani daɗi ya lulluɓe sassan jikinta,tabbas tafi kowa dacen samun masoyi,duba da yadda yake sonta. Shuru tayi tana wasa da hannayenta,yayin da hisham ya tsureta da shanyayyun idanuwansa yanason jin amsarta. A hankali tace"ya hisham,naji daɗin bayaninka,sosai kuma na gamsu, kuma batun yanzuba na yaba da natsuwa da hankalinka Allah yashige mana gaba na karbi soyayyarka da dukkan zuciyata"ta ƙarasa maganar cike da jin kunya,yayin da shi kuma ya sauke wata ajiyar zuciya gami da yiwa Allah godiya. Daga haka suka shiga hira irin ta masoya,har zuwa lokacin sallar la'asar ya fita zuwa masallaci ya gabatar da sallah sannan yadawo tai masa iso gun mahaifiyarta.suka gaisa tasa musu albarka gami da fatan alkha'iri. A garin ya kwana a tahir hotel wanda yafi kusa da gidan nasu safiyya,gari na wayewa ya kamo hanyar kaduna bayan sunyi sallama da safiyyarar kamar karsu rabu. Koda ya iso gida cike da nishaɗi inna ta tarbeshi yabata tsaraba sannan ya wuce ɗakinsu,dan ya ɗan huta. Koda haisam yadawo be ɓoye masa yadda sukayi da safiyyaa ba ya sanar da shi.sosai yatayashi murna gami da yimasa fatan alkhairi. " " *Wacece safiyya ishaq?* Safiyya ishaq haifaffiyar unguwar nasarawa dake cikin birnin kano,su biyar ne agun iyayensu duka mata,itace autarsu,gaba ɗayan su yan boko ne, gidan shiyasa sukevda wayewa sosai ko kaɗan basu da duhun kai. Mahaifinsu ya rasu tun safiyyaa na yarinya,sunan mahaifiyarsu hajiya Hadiza suna kiranta Ammi,yayyanta mata huɗu kuma duk sunyi aure,se ita safiyyar cekawai ta rage agabanta. Suna da rufin asiri dede gwargwado,dan mahaifiyarsu 'yar kasuwa ce,dan wani lokacin har dubai take fita ta saro kaya.Tana ƙaton shago da take siyar da abayoy da,atamfofi da lace,sannan ita malamace a jamia. Yawancin 'yan unguwarsu ƴaƴan mace suke ce musu,sabida kawai su wayayyune,ga ilimin boko,dan safiyya degree gareta afannin mass com,haka sauran yayyanta. Wannan kenan Soyayya tayi ƙarfi sosai tsakanin hisham da Safiyya,wanda kowa a danginta yasan da soyayyarsu, Saɓanin shi hisham ɗin in banda haisam ba wanda yasan da batun dan inna har yau batasan labarinba.Kullum burinta suo babban kamu dan su fantama Mahaifiyar safiyya ce ta buƙaci ganin hisham,bayan yaje ne ta buƙaci da ya turo iyayensa a tsaida magana,dan baze yiwu ayta soyayta kawai manya basu shiga ba. Jiki asanyaye modibbo yabaro kano zuwa gida. Gaba ɗaya jinshi yake kamar wani mara lafiya,har zuwa dare hisham beda sukuni.Shi kaɗai yasan me yakeji,tsoronsa taya ze tinkari inna da batun auran safiyya. Koda suka zo cin abinci ma shi kasa ci yayi sabida tunanin da yay masa yawa.Se juya cokali yake haisam ne ya kai dubansa garesa cike da kulawa yace"ɗan uwa gidan su safiyyane suka buƙaci katuro iyayenka ko?"da sauri hisham ya waigo yana gyaɗa masa kai bakinsa har harɗewa yake yace"wallahi haisam shine yasa kaganni cikin wannan tashin hankalin,na rasa mezan cewa inna"ya ƙarasa maganar cikin rauni. "Ka kwantar da hankalinka,insha Allahu kai da safiyya zaku mallaki juna,kazama jajirtaccen namiji komai zezo da sauƙi yanzu ka bani wuƙa da nama komai ze dede ta"cewar haisam yana murmushi. "Na baka haisam kuma nasan zaka iya,pls ka taimaka"cewar hisham cike da damuwa. Ƙarasa cin abincin sukayi sannan haisam ya miƙe ya fice zuwa ɗakin inna dake zaune kan tabarma tana jin radio. Shigowar haisam ɗin ce tasa ta kashe radion ta yalwata murmushin kan fuskarta tace"haisam,ya akayine?"ta faɗi tana gyara zamanta. Guri yasamu kusa da ita yazauna sannan yatattaro dukkan natsuwarshi sannan yace cikin tattausan lafazi. "Inna Alamu sun gwada kamar baki,rike shekarun da kika haifemu ba ko?"ya wurga mata tambayar gami da bin ta da ido. Duka ta kai masa gami da faɗin"kaci gidanku haisam,ni ɗince bansan shekarunku ba?to kuna cikin shekara ta talatin,badia kuma ashirin da huɗu"cewar inna ."good,"cewar haisam gami da gyara zamanshi sannan yaci gaba da cewa"Inna keda baba kuna da shekaru nawa nawa kuka auri juna?" Cike da mamaki ta kalleshi,tana son ta gano manufar tambayar tashi amma ta kasa dan haka amsa ta bashi da cewa"babanka ashirin da biyar ni sha biyar,menene ya faru ne haisam da irin wainnan tambayoyi haka,? Wasu hawaye ne suka biyo fuskarsa masu zafi na tausayin kansu ,sannan yace"Inna yanzu shekarar mu talatin da haihuwa,in kin mantane zan tuna miki,nida haisam mun jima da balaga,mu baligai ne inna masu cikakkiyar lafiya,muna buƙatar mace akusa damu ahalin yanzu ki taimaka kibar hisham yayi aure da wacce yake so ko hankalinshi ze kwanta,yaƙi sanar dakene dan kar ki ƙi barinsa"yaƙarasa maganar cikin kuka. Baki bud'e inna take kallon haisam,sabida tsananin mamakin maganganun nasa.da kyar ta iya ce masa. "Wacece wacce yake son ?aina take,'yar gidan wacece?"sune tambayoyin inna. "Sunanta safiyyaa ishaq,'yar garin kano ce,sun haɗu a bikin kabeeru da mukaje marabar rido suna matuƙar ƙaunar junansu"cewar haisam ba tare da tsoron komai ba. Shuru inna tayi tana nazarin maganar kamin tace"to naji ka amsomin adireshin gidansu zansa abincikamin tarbiyarta insun dace se ayi"cewar innar ba tare da damuwar komaiba. Rungumeta haisam yayi yana me nuna farincikin shi afili yace "mungode inna"yatashi yafice dagudu zuwa ɗakinsu yana shiga yaywa hisham albishir sosai yay farin ciki da jin cewa inna ta yarda yay aure. Ita ko inna wani malulun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarta jin cewa hisham nada wacce yakeso batare data sani ba,duba da irin uban kuɗin datake kashewa gurin malamai duk dan suyi farin jini,amma shine koda wasa be taɓa shaida mata yayi budurwarba. " " Wayarta ta janyo ta nemo wata numba ta danna kira,ba'a jima ba aka d'aga,koda aka d'aga ba gaisuwa ba komai tace"hajiya sabuwa ina cikin matsala"daga can b'angaren wacce aka kira da hajiya sabuwa tace " inna wacce irin matsala kuma?" "Yaronki mana hisham nason sani a masifa,wai wata yakeso a kano,wallahi hankalina yanzu haka atashe yake,sabida kinfi kowa sanin fɗi tashin da mukei akan yaranmu ade samu su auri ƴaƴan manya" Salati hajiya sabuwa tayi sannan tace "ke ko kina wanne gangancin hakan ta faru,?"kwashe duk yadda sukayi da haisam tayi ta sanar da ita,Sannan ta k'ara da cewa"wallahi ba abinda yafi d'agamin hankali se hajiya kulu,kinfa san komai yanzu in taji da wanne ido zan kalleta ni inna nashiga uku,kina ganide agabanki akayi komai,lokacin da mukaje nidake anso bashi agurinta na miliyan goman da wannan sabon malamin da ya damareni yay min alƙawarin da sunyi amfani da maganinsa har ƴar shugaban ƙasa ma zasu iya aura ɗinnan da kika rakani naje gunta ta bani mukayi yarjejeniya"cewar inna cikin tashin hankali. "Ay baki shiga uku ba ma se in taji labarin"cewar hajiya sabuwa. "Sabuwa kwakwalwata ta cushe ki bani shawarar abunyi wallahi ji nake kamar zanyi hauka"cewar inna cikin tashin hankali ,dan damuwarta in hajiya kulu tace ta biyata kuɗinta ta inda zata samosu tunda sunyi da ita cewar in lokacin biyan kuɗin yayi bata kawoba to cikin ƴaƴanta maza dole ta aurawa ɗaya ita hajiya kulun,kuma ta amince mata ahaka. "Dole ki fito ki sanar dasu gaskiyar lamari,cewar akwai bashi tsakaninki da hajiya kulu,wanda kukayi yarjejeniyar zata baki bashin wanda in lokacin biya yayi baki biyaba,cikinsu zata zaɓi guda ta aura ,dan haka tun wuri ya hak'ura da wancan yarinya ba samunta zeyi ba tunda bakisan cikinsu wanda ita hajiya kulun zata zaɓaba,amma inkin k'i to ko zaki shirya yin aman duk kud'in data baki"cewar sabuwa. Gwauron numfashi inna taja,sannan tace"zan sanar dashi sabuwa insha Allahu komai ze tafi dai-dai"sallama sukayi takashe wayar.tana saka abubuwa da yawa acikin ranta. A daren haisam yakawo mata address d:in gidan su Safiyyaa ba tare da tunanin komai ba. Washe gari tun asuba inna ta fice daga gida bata zame ko ina ba se kano,bata sha wiya ba ta gano gidan,kallo daya taiwa gidan ta raina arzikinsu,makwabta ta dan tambaya game da gidan nan ko aka labarta mata cewa su safiyyan ƴaƴan macene. Inna de bata baro garinba seda tai arba da safiyya,inda munafikin dake mata bayaninsu ya nuna mata ita lokacin ta rako k'awarta k'ofar gida. Sam safiyyan bata yimata ba,dan haka tasha alwashin raba wannan soyayyar kota halin k'ak'a.Dan bazata yarda ta zamo silar jefata adamuwaba. Bata iso gida ba se k'arfe goma na dare lokacin su hisham sun fita nemanta sabida basu ganta ta dawo ba.Hankalinsu atashe an duk sun tambayi maƙwabta kowa yace batazoba. Haisam ne yafara ganinta da sauri ya matsa kusa da ita yace"inna ina kikaje kika jima haka duk kinbi kin d'aga hankalinmu"ya fad'i cikin yanayi na damuwa. Raɓawa tayi ta shige cikin gidan ba tare data bashi amsa ba,haka suka biyota abaya zuwa cikin gidan. Kan tabarma tahau ta zauna sannan tace "wash Allah na wallahi na gaji daga kano nake gidan su Safiyya budurwar hisham"ta basu amsa ba tare da tunanin komaiba. Azabure suka kalli juna sannan dukansu suka zauna gefen tabarmar suna fad'in"Gidan su Safiyya kuma inna? To kikaje yin me agidan nasu?" Turo d'ankwalinta gaba tayi sannan tadan gyatsine fuska tace"tace eh fa gidansu,to ko laifine zuwan nawa?" Asanyaye suka girgiza mata kai. Ci gaba da magana tayi cikin isa da k'asaita tace"hisham sam wannan ƴar macen bata dace da kai ba kuma ba zaka aureta ba,bama wannan ay ka jima da sanin cewa ga kalar matan da nikeso nike fatan ace kun aura,da zakaje ka jajibo mana ƴar matsiyata,dan haka wallahi na yanke wannan alaƙar,kuma ina so kasani safiyyaa ko wata shigenta bata da matsugunni agidanka idan har nice na haifeka"cewar inna tana nunashi da hannu. Agigice hisham yake kallon haisam wanda shima shi yake kallo,bakinsu har hard'ewa yake wajem tambayar"inna me yay zafi haka? dan Allah karki datse wannan soyayyar" Gyara zama tayi tace"inaso dukankunku sani bawai ina narkawa malamai kuɗi bane dan inadasu kan suyi muku aykin farin jini,duk abinda nakeyi bashin su nake ciyowa,kuma inda ake ban bashin akwai sharaɗin da aka bani gameda duk kuɗin danake karɓowa,wanda in har ban cikaba to rayuwata da taku zaa saka a matsala"cewar inna cikin damuwa Hankali tashe hisham yace"inna shi bashinne ze hana aurena da safiyyar?"ya tambaya muryarshi na rawa. "eh hisham shine ze hana sabida hajiyar tacemin in har ban biyata kuɗin da mukayi zan bata ba to dole acikinku ɗaya seya aureta,kagako bansan wa zata zaɓa acikinku ba shiyasa dole ayi haƙuri dama kowacce macece"cewar inna. Ba hisham ba hatta haisam seda ya girgiza da jin bayanin na innar. "wacce hajiyace wannan inna?"cewar haisam hankali atashe. "hajiya kuluce"cewar inna. "Inna wai Hajiya kulu Babar su jagudu?"cewar hisham bakinsa na rawa. Murmushin ƙarfin hali inna tayi sannan tace"kwarai kuwa ita hisham". Zamewa sukayi azaunen da suke suna ƙoƙarin faɗuwa,sabida kaɗuwar da sukayi. "dan haka cikinku dole ɗaya ze aureta dan banida miliyan goman sa take bina,dan ko gidan nan aka siyar da mashinanku bazuyi rabin kuɗin bama,"cewar inna. "amma innakinyi kuskure,taya zakije kici bashi har na miliyan goma bayan kinsan mu ko ke bamu da hanyar samun irin wannan kuɗaɗen,innalillahiwainnailaihirrajiun"cewar haisam kamar ze rufe innar da duka sabida takaici. Shuru inna tayi dan se yanzune take danasanin cin bashin tunda taga yadda hankalin biyullen nata ya tashi. Cikin kuka hisham ya fara magana"inna tabbas bamuda kuɗin da zamu biya mu fanshi ƴencinmu da kika siyarwa da hajiya kulu,sabida bazamu zuba ido munakallo awulaƙanakiba,dan haka amatsayina na babba ni na amince a auramin itan dan biyan bashin da kika ciwo"cewar hisham cikin kuka. Azabure haisam ya ruƙo kafaɗunshi yana jijjigashi yace"kayi haukane hisham,hajiya kulufa,me zakayi sa ita,ita safiyyarfa,pls ka dawo hayyacinka kar ka yarda ka auri annan watsatstsiyae matar,ama taba inna bashinne dan tasamu ɗaya acikinmu tunda tasan inna bata da hanyar biyanta kuɗi me yawa haka,dan Allah karka bari ta rsa maka mafarki"cewar haisam cikin matsanancn kuka. Rungumeshi hisham yayi yana faɗin"na haƙura da safiyyar haisam ba rabona bace,dole mu biya wannan bashi da inna taciyo" "Inna tun wuri ki sauya tunani kamin hakkinmu ya waiwayeki,taya yana saurayi zaki had'ashi aure da mace tsohuwar ƴar bariki,wanne irin son kai ne wannan inna?Mu muka ce ki ciwo bashin,koko mun san kin ciyo,amfanin me kuɗin sukayi mana da zaace mu zamu biya?"cewar haisam azafafe yana kuka kamar ranshi ze fita. Afusace inna tayo kanshi da fad'in"ka iya bakin ka haisam wallahi inka tunzurani da hajiya sabuwa zan had'a ka kaima,ka barni inji da abinda yake damuna mana".Ta faɗ cikin ƙaraji itama hawaye na biyo idanunta. "Ko hajiya tsohuwace inna ni nafi ƙarfin kiyimin haka shima hisham tausayinsane yay yawa da nine wallahi sede duk abinda ze faru ya faru,amma wallahi bazan yarda ba"cewar haisam wanda yakejin ze iya komai kan wannan abu da inna tai musu. Kanshi inna tayi tana zazzaga masifa tana kai masa duka da kyar hisham yasamu ta natsu,tsugunawa yayi a gabanta yana kuka yace."Inna ta son da nike miki yazarce na kowa aduniya,nafi k'aunar farin cikin ki kan nawa innata,in har aurena da hajiya kulu ze saki farin ciki,ze yaye miki duk wata damuwarki, inna ta na amince kisa a daura,Allah ya bani hak'urin miki biyayya,amma ina roƙonki haisam kibarshi ya zaɓo kalar macen da yakeso da kanshi dan Allah"ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka. " " "Ka samawa kanka lafiya"cewar inna tana huci. Mik'ewa tayi tanufi d'akinta harta kai bakin k'ofa ta juyo tacewa hisham,"gobe da k'arfe sha biyu na rana Hajiya kulu zata shigo gari,kuma nasan zeyi wuya bata nemeniba dan haka ka zama cikin shiri in naje mukayi magana to zata iya zuwa zance gunka saura inji ka mata ba daidaiba in tazo"ta faɗi ranta aɓace. K'ara rusunawa yayi idonshi na fitar da kwalla yace"to inna ta zaki sameni be biyayya insha Allahu"ya faɗi muryarsi na rawa. Shigewa d'aki tayi ba tare data sake bi ta kansu ba. Daga hisham har haisam d'in ba wanda yayi yunkurin motsawa yabar gurin sunanan tsugune har aka kira sallar asuba,dukansu kuka suke. Kiran sallar ne yatashesu agurin sukai alwala suka wuce masallaci. Koda akaje sujjadar k'arshe hisham be dago da wuriba,rushewa Allah yayi da kuka yana fad'in. "Ya Allah nayi biyayya,ya Allah nayi biyayya ya Allah nayi biyayya,kadubeni da idon rahama ka sauk'ak'amin rayuwata,ka zabamin innata amatsayin mahaifiya Allah banyi fushi ba ya Allah in hajiya kulu ka zab'amin amatsayin mata Allah kar kasa nai fushi,nagode ma Allah kadubeni"😭yak'arasa addu'ar cikin kuka,sannan ya d'ago. Koda suka baro masallaci gida suka dawo haisam d'akinsu yawuce kai tsaye,dan beson ganin inna. Hisham ko d'akinta ya wuce da sallamarshi ya shiga d'akin,dakyar ta amsa masa,murmushi ya k'irk'iro sannan ya k'arasa gurinta kamar ba abinda ke damunsa ya tsuguna agabanta yace"innata barka da asuba da fatan kin tashi lafiya?"ya faɗi yana kallonta Ba laifi tadan saki fuska tace"lafiya lau"daga haka bata sake cewa komai ba,se daga bisani zuwa can tace. "In kace zaka biye wa haisam asara zakai tayi arayuwarka,kaga de na farko hajiya kulun nan y'ar majalisa ce, gata da kud'i ga hanyoyi,kaga in ka aureta har kasar waje fita zatai da kai kaima kasamu ka murmure,duk abinnan da nikeyi dan ku nakeyi ba kuma dan bana sonku ba amma kanaso ka biyewa wancan shashashan ku rasa duka"cewar inna tana watsa masa harara. Murmushi yayi afili yayinda zuciyarshi ji yake kamar wutar matatar man fetur aka kunna mata,dakyar yace"hakane innata Allah yashige mana gaba" Shuru ne yabiyo yar hirar tasu kana daga bisani ya mik'e ya fice zuwa d'akinsu. Atsaye yasamu haisam yana kai gouro yana kai mari,cikin k'unar rai haisam yace masa"nufinka ka amince da auran waccan tsohuwar guzumar kabar safiyya?"ya faɗi yana kallon fuskarshi. "Kusan hakane haisam,tunda haka inna take so dole in mata biyayya,safiyya kuma na hak'ura da ita,tunda inna bazata bari in aureta ba"suna cikin maganar wayarshi tai kara da sauri ya karasa k'an wayar ya d'auka,dan yasan me kiran tun daga sautin wayar. Safiyya ce,anatse suka gaisa sannan yace mata"baby ta dama ina shirin kiranki se gashi kin kira,dama wata magana nakeson sanar dake ina fata da addu'ar Allah yasa kimin fahimta me kyau"cewar hisham muryarsa na rawa. Dagacan b'angaren tace"insha Allahu ya hisham zan fahimceka nayi alk'awari"cewar safiyya Daga haka hisham ya kwashe komai ya sanar da ita,ayko ita kuka shi kuka,da kyar yashawo kanta tai shuru,sannan tace cikin dusasshiyar murya "na yarda da kai hisham fiye da kaina,karka damu kaje kai auranka safiyya takace ya hisham shekaru d'ari matuk'ar kana raye kaje ka dawo safiyya ina gida zaman jiranka,"tana kaiwa nan ta kashe wayarta cikin kuka. Koda ya kirata ta kashe wayar gaba d'aya tsugunawa yayi agurin yana kuka kamar mace,da kyar haisam ya rarrasheshi yay shuru,zuga shi ya shiga yi kan ya bijirewa auran amma ina fafur yak'i yarda haka ya ƙyaleshi. Tun sha d'aya da rabi nasafe inna tasa hisham ya shirya ya zauna zaman jiran hajiya kulu,se fad'a take masa kan kar ya sake hajiya kulu ta gano dole tai masa.ba,a son ransa ze aureta ba.Shide ba baka se kunne jinta kawai yakeyi. Inna ficewa tayi zuwa gidan hajiya kulu,tai mata bayanin bata da halin biyanta kuɗinta amma cikin ƴaƴanta ta yanke shawarar aura mata hisham amadadin kuɗin nata kamar yadda suka tsara. Hajiya kulu wani farincikine ya kama zuciyarta,sanda inna ke sanar mata da batun bata ɗanta ta aura,yaran ake tashen kyau kamar larabawa,tabbas tayi babban kamu cikin sauƙi. Hajiya kulu amincewa tayi harda kawo wasu kuɗi masu tsoka taba inna sannan tace mata anjima zatazo taga yaron,ayko inna godiya take bata wasaba ta baro gidan ranta fess,ta dawo gida. Sunanan zaune hajiya kulu ta k'araso acikin wata farar mota k'irar benz2026,yan rakiyarta kuma amotoci guda biyu na jamian tsaro kallo d'aya zakai mata kasan kud'i sun zauna ajikinta,doguwace fara ga jiki,ba laifi tana da kyan fasali,bakinta kwai hak'orin maka guda biyu fari da gold,sede kallo d'aya zakai mata kasan gogaggiyar y'ar duniyace,hajiya inno magaji kenan y'ar majalisa me wakiltar karamar hukumar kaduna south a Abuja. Cikin takun isa da k'asaita ta shigo cikin gidan yayin da y'an sandan dake kula da ita suka tsaya a waje,PA d'inta ce kawai ta biyota d'auke da jakarta. Inna har tuntube take gun sauri duk'awa ta gaishe da hajiyar,da kyar ta amsa mata sannan tace"ina mijin nawa?" Akid'ime hisham shima ya zube agabanta kamar yadda yaga inna tayi cikin gigita besan sanda yace" gani umma"ba "What!!!wacece ummar taka,haba ina laifin ma ka kirani baby ko honey"cewar hajiya kulu Inna har k'warewa takeyi yayinda ta waigo gun hisham tana fad'in"baby sunanta daga yau" "To inna naji"cewar hisham muryarsa na rawa "Taso muje gidana mayi hirar acan dan nan warin kwatar can har yafara damuna,"cewar hajiya kulu sanda ta juya zuwa waje,ba musu hisham ya mik'e yabita a baya. " " Gidan baya ya shiga inda take driver yajasu zuwa gidanta daya gaji da had'uwa. Awani falo na musamman ta saukeshi,kan kace me ancika masa tebur da abinci kala kala. be iya shan koda ruwan gidanba bare. Wani abu waishi abinci. Hajiya kulu ita tai ta surutunta yayinda shi ko daga uhm se uhm uhm,har zuwa la'asar suna tare afalon seda ya gaji yace mata. "To ni zan wuce" Shagwab'e fuska tayi tana fad'in"kai haba de tun yanzu?,koda yake rana ita yau ay kadawo gidanma gaba d'aya da zama naga ta saurin tafiya" Murmushin ƙarfin hali kawai yayi,danshi ya k'osa yabar gurin.mik'ewa tayi tashiga d'akinta sannan tafito hannunta d'auke da wata jaka, tamik'a masa tace "Gasunan ba yawa,ka raba gida biyu ka bada sadaki da rabin rabin kuma ka sallami gidanku" "To nagode Allah saka da alkha'iri"daga haka ta rakoshi har bakin k'ofar falon tayi ya fice ya shiga motar da zata mai da shi gida,ita kuma ta koma ciki. Koda yazo gida be samu inna a gidan ba,dan haka d'akinsu yashiga,jakar data bashi ya bud'e,kud'i ne aciki koda ya zazzagosu maira milyan biyu ne aciki. Beyi mamaki ba dan yasan tafi k'arfin kud'in. Yana nan zaune haisam yashigo d'akin,da kud'in yay tozali da sauri ya k'arasa gun d'an uwan nasa yace"D'an uwa wannan kud'infa?" "Umma kulu ce ta bani"cewar hisham batare daya san me yace ba. Wata mahaukaciyar dariya haisam ya fashe da ita har yana rik'e ciki yace"wallahi fa sede umma kulun fa kam," Se alokacin ya tuna da sunan daya kirata,shima murmushin yayi. "'Wannan kud'in na menene hisham?,ina fatan ba seda kanka zakai agareta ba?"cewar haisam cikin yanayin tuhuma. Gyara zama hisham yayi sannan yace"haisam ko in ansa ko kar in ansa inna ta riga ta gama siyar dani to ya zanyi?"Nande yakwashe duk yadda sukayi da ita ya sanar dashi. Shuru haisam yayi yana jinjina lamarin,tabbas yasan gaba akwai kallo.afili kuma seya nuna shi beji dad'in amsowar da yayin ba. Fafur haisam ya hana hisham ba inna kud'in inda ya shawarceshi daya tara su,kar ya sake ya tab'a sabida gaba. Da shawarar yay ayki nan take ya ware miliyan guda na sadaki, d'ayan kuma yaba haisam d'in ya ajiye masa. Haka hisham yaci gaba da jewa gun inno hira,badan ranshi yaso ba.Sedan haka nna ta tsara masa. Sati guda inna tasa na auren dan haka dangin babanshi ta aykawa,abunka da k'auye da kud'i basu tsaya bin ba'asi ba suka d'ungumo kaduna dan d'aurin auren. Ta b'angaren hajiya kulu har gyaran jiki tayi dasu magungunan mata dan megidan yaji tsab. Haka tasashi dole sukaje hoton pre wedding,goɗai goɗai da ita haka taita rungumarsa ana musu hoto, Ba laifi sunyi kyau sabida hajiya kulu nada kyau. Kan kace me duk ta d'ora su akan social media,nanko akaita ce wa "wani yay wuf da uwar wasu" Akwatina biyar ta cika mishi da kayan maza nagani na fad'a masu tsadar gaske,duk an d'inkosu d'inki na zamani.Daya dace da zubin jikinshi. Koda drivernta ya kawo masa ya bud'e ya gani kayan sun burgesa.Amma acan cikin zuciyarshi jinsa yake kamar me shirin zuwa lahira ko kad'an be murna da auren... " " Har bakin k'ofar falon direban ya kawo shi,jiki asanyaye ya bud'e k'ofar motar ya fita. Ya jima tsaye bakin k'ofar falon kamin ya murd'a k'ofar yajita abud'e ya shiga da sallamarshi.ba kowa a falon dan haka guri ya samu kan kujerun falon ya zauna. Shuru shuru ba wanda ya fito shi kuma besan kan gidan ba dan haka nan kan kujerar yay zamanshi. Hajiya inno na falon sama zaune taji motsin shigowarshi,to ta d'auka ze hauro saman jin shurun tayi yawane yasa ta sauko da kanta, Akan kujera tasameshi zaune,da sauri yakai dubansa gunta ya mik'e da sauri yad'an rakub'e agefen kujerar. .ita ko cikin takun isa da k'asaita ta iso gabanshi fuskarta d'auke da murmushi,tace "shine baka hauro sama ba ka zauna anan?"ta faɗi

Chapter 2 of 3